Isa ga babban shafi
Najeriya

Ma'aikatan Jiragen Kasa A Najeriya Sun Fara Yajin Aiki Na Kwanaki Uku

Ma'aikatan Jiragen kasa a Najeriya sun fara yajin aiki na kwanaki uku na gargadi kafin su tsunduma yajin aiki da babu adadin karewa sai an biya  bukatunsu.

Wani jirgin kasa a Oshodi Lagos Najeriya
Wani jirgin kasa a Oshodi Lagos Najeriya AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI
Talla

A yau Alhamis suka fara yajin aikin don nuna rashin jindadinsu game da rashin samun albashi mai kauri da ya dace da aikin da suke yi.

Ma’aikatan za su yi yajin aikin na kwanaki uku daga yau Alhamis 18 ga wata zuwa Asabar 20 ga watan Nuwamba 2021.

Ma'aikatan na bukatar Gwamnatin kasar ta gyara masu tsarin albashi da sauran hakkokinsu saboda bai dace su ci gaba da karban kudaden da ake biyansu ba yanzu.

Ministan Sufuri na kasar Rotimi Ameachi ya gayyaci kungiyoyin kodago ranar Asabar da ta gabata don warware takaddamar amman kuma taron bai yi wani tasiri ba.

Kafin wayewar gari yau Alhamis jiragen kasa a fadin Najeriya suka dakatar da ayyukan na su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.