Isa ga babban shafi
Najeriya

Hatsarin kwale-kwale ya hallaka 'Yan Mata 7 a Jigawa

A Najeriya wasu ‘Yan mata 7 ne suka nutse a ruwa bayan da wani kwale-kwale da suke cikin ya kife a jihar Jigawa da ke arewacin kasar.

Wasu dake cikin kwale-kwale a Kogin Neja
Wasu dake cikin kwale-kwale a Kogin Neja Getty Images/Shanna Baker
Talla

Kakakin ‘yan sandan jihar Jigawa Lawan Shiisu yace ‘Yan mata 10 masu shekaru tsakanin 10 zuwa 12, na kan hanyarsu ta komawa gida cikin dare bayan wani biki kafin iftila’in ya rutsa da su.

"An ceto uku daga cikinsu yayin da wasu bakwai... aka ruwaito sun mutu," in ji Shiisu.

‘Yan matan, wadanda suka kosa su koma gida da karfe 12:15 na dare, sun yanke shawarar jan kwale-kwale da suka samu a bakin kogin da kansu ba tare da wani matuki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.