Isa ga babban shafi
Najeriya - Filato

'Yan bindiga sun kashe mutane 10 a Filato

Rundunar ‘yan sanda a Filato da ke Najeriya ta ce gungun ‘yan bindiga sun kai hari a wani kauye a jihar, inda suka kashe mutane 10 tare da kona gidaje akalla 30.

Wani yanki na garin Bokkos a jihar Filato.
Wani yanki na garin Bokkos a jihar Filato. GIANLUIGI GUERCIA / AFP
Talla

Yayin karin bayani kan tashin hankalin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Filato Ubah Ogaba, ya ce ‘yan bindigar sun kai farmakin ne kan kauyen Te’egbe da ke karamar hukumar Bassa.

Shi kuwa mai magana da yawun al’ummar yankin, Davidson Malison, kuma wakilin kungiyar ci gaban kabilar Irigwe, ya dora alhakin harin kan Fulani makiyaya.

Sai dai tuni kungiyar makiyayan ta Miyatti Allah ta yi watsi da zargin.

Jihar Filato dai ta kwashe shekaru tana fama da rikicin makiyaya da manoma da ke rikidewa zuwa na addini, ko da yake a wannan karon jami'an tsaro sun danganta hare-haren na baya-bayan da masu neman tada zaune tsaye a maimakon rikicin addini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.