Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TATTALIN ARZIKI

Buhari zai halarci bikin baje kolin 'EXPO 2020 Dubai'

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yau zai bar kasar zuwa Dubai dake Daular Larabawa, inda ake saran ya halarci bikin bajen kolin da aka yiwa lakabi da ‘EXPO 2020 Dubai’.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

Sanarwar da mai magana da yawun sa Femi Adeshina ya rabawa manema labarai tace bikin na bana zai baiwa Najeriya damar shiga jerin kasashen duniya sama da 190 domin kulla sabbin yarjeniyoyin kasuwanci da zuba jari domin gina makoma mai kyau ga al’ummar kasar a shekaru masu zuwa.

Adeshina yace bikin zai kuma baiwa tawagar Najeriya damar bayyanawa duniya irin ci gaban da wannan gwamnatin ta samu wajen bunkasa tattalin arzikin kasar a cikin shekaru 6 da suka gabata da kuma irin shimfidar da tayi wajen baiwa masu zuba jari damar zuwa kasar domin cin gajiyar shirin.

Mahalrta taron zuba jarin Najeriya a Paris ke sauraron shugaban kasa Muhammadu Buhari
Mahalrta taron zuba jarin Najeriya a Paris ke sauraron shugaban kasa Muhammadu Buhari © Nigeria presidency

Ana saran shugaba Buhari ya ziyarci runfunan da aka warewa kasar domin baje kolin ta a ranar juma’a da karbar baki tare da masu zuba jari da kuma ganawa da Sarki Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan da Yariman Abu Dhabi kuma mataimakin babban kwamandan sojin kasar Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum.

Sanarwar tace a ranar asabar shugaba Buhari zai zama babban bako na musamman wajen taron baje kolin da Najeriya ta shirya a karkashin ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da kuma zuba jari.

Shugaba Buhari wajen taron zuba jarin da akayi a watan Oktoba a Paris
Shugaba Buhari wajen taron zuba jarin da akayi a watan Oktoba a Paris © Nigeria presidency

Adeshina yace daga cikin wadanda zasu raka shugaban a wannan tafiyar akwai ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama da ministan kasuwanci da zuba jari Otunba Adeniyi Adebayo da ministar kudi Zainab Shamsuna Ahmed da ministan tsaro Janar Bashir Magashi da na sufurin jiragen sama Hadi Sirika da ministan noma Muhammad Abubakar.

Sauran sun hada da ministan lafiya Osagie Ehanire da na sadarwa Isa Ali Pantami da na tama da karafa Olamilekan Adegbite da mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro Janar Babagana Monguno.

Adeshina yace ana saran shugaban ya koma Najeriya ranar lahadi mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.