Isa ga babban shafi
Najeriya-Lafiya

Kwalara ta fi kashe 'yan Najeriya fiye da Korona - NCDC

Hukumar Yaki da Cutuka Masu Yaduwa ta Najeriya ta bayyana cewa, cutar kwalara ta fi kisan jama’a fiye da annobar Covd-19 musamman a wannan shekara ta 2021 a kasar.

Wasu masu jinyar cutar Kwalara
Wasu masu jinyar cutar Kwalara Reuters/St-Felix Evens
Talla

Darekta Janar na  Cibiyar ta NCDC, Ifedayi Adetifa ya bayyana cewa, Najeriya ta samu adadin mutanen da ya zarta  dubu 3 da 600 da suka rasa rayukansu a dalilin annnobar amai da gudawa ko kuma kwalara a cikin watanni 11 da suka gabata.

A game da annobar Covid-19 kuwa, kimanin mutane dubu 2 da 977 ne suka rasa rayukansu tun daga  farkon shekarar bara zuwa wannan lokaci, kamar yadda Mista Adetifa ya yi karin bayani.

Jami’in na hukumar NCDC na bayani ne a yayin wata hira da ya yi da kafar Talabijin ta Channels, inda ya yi  bayani game da sabon nau’in cutar Korona da ake kira Omicron da ya bulla a Najeriya.

A cewarsa, yanzu haka sun dukufa ne wajen takaita yaduwar cutar kwalara duk da cewa, a halin yanzu, mutane sun fi karkata hankulansu kan annobar Covid-19.

A bangare guda, Mista Adetifa ya  kara a cewa, tuni suka fara kintsawa domin tunkarar kakar ciwon sankarau, yana mai cewa, sun tanadi ma’aikata tare da horas da su don gudanar da aikinsu na wayar da kan al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.