Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun hallaka matafiya kan hanyar Kaduna -Zaria

A Najeriya an samu mutuwar matane a wani hari da ‘yan bindiga suka kai tareda bude wuta a kan matafiya a kan  hanyar Kaduna-Zaria,

Hanyar da tashi daga birnin Abuja zuwa Kaduna.
Hanyar da tashi daga birnin Abuja zuwa Kaduna. Daily Trust
Talla

Kusan watanni biyu kenan da 'yan bindiga suka haddabi arewacin  Najeriya, jama'a na cikin damuwa,an dai fahimci cewar ‘yan bindigar sun bude wuta a kan matafiyan tareda tilastawa direbobin  tsayawa a kan hanya, abinda ya basu damar kwasar fasinjoji da dama .

Harabar filin jiragen sama da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya.
Harabar filin jiragen sama da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya. © Twitter / @GazetteNGR

Majiyoyi a Najeriya sun ce wannan farmaki ya faru ne a kofar Gayan dake wajen garin na Zaria kuma sun fara aika aikar ce tun misalin Karfe 8  na daren Litinin.

Masu zanga-zanga sun kuma kona tayoyi akan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna
Masu zanga-zanga sun kuma kona tayoyi akan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna © The Guardian Nigeria

Yan bindigar dai sun kwasi mutane da dama sannan sun harbe wasu da dama kana wasu kuma suka tsere. Hukumomi tareda hadin gwiwar jama'a na kokarin tattance mutanen da 'yan bindigan suka yi awon gaba da su,yayinda mutanen da suka samu rauni aka garzaya da su asibiti.

Rahotannin baya-baya na nuni cewa,jami'an tsaro sun isa yankin ba tareda bada karin haske ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.