Isa ga babban shafi
Najeriya - Nijar

Dakarun Najeriya da Nijar sun kashe 'yan ta'adda da dama Tafkin Chadi

Sojoji 6 da mayaka masu ikirarin jihadi akalla 22 ne suka mutu, yayin fadan da aka gwabza tsakanin sojojin Najeriya da na Nijar da kuma ‘yan ta’addan gefe guda, a Yankin Tafkin Chadi.

Wasu sojojin jamhuriyar Nijar da ke taimakawa Najeriya wajen yaki da kungiyar Boko Haram.
Wasu sojojin jamhuriyar Nijar da ke taimakawa Najeriya wajen yaki da kungiyar Boko Haram. AFP - PHILIPPE DESMAZES
Talla

Sanarwar da rundunar hadin gwiwar kasashen Najeriya, Nijar, da Kamaru da kuma Chadi ta fitar a ranar Juma’a, ta ce dakarun nata sun samu nasarar ce, da taimakon jiragen yaki da kuma tallafin Amurka, wajen kaddamar da farmakin da rundunar ta rika kaiwa kan ‘yan ta’adda tsawon makwanni 3 a bangaren iyakar Najeriya.

Rundunar ta MNJTF ta kara da cewar dakarun ta da suka kwanta dama yayin fafatawar ta baya bayan nan sun hada da sojojin Najeriya 4 da na Nijar 2, yayin da wasu 23 suka jikkata, a lokacin farmakin da suka kawo karshensa a ranar Talatar da ta gabata.

Tarihi dai ya nuna cewar tun shekarar 1994 aka kafa ginshikin farko na rundunar hadin gwiwa ta MNJTF, inda a waccan lokacin ta kunshi sojojin Najeriya kawai, wadanda aka dorawa alhakin murkushe barazanar tsaro ta barayin shanu akan iyakokin kasar daga bangaren arewacinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.