Isa ga babban shafi
Najeriya

Allah ya yi wa Bashir Tofa rasuwa

Tsohon dan takarar shugabancin Najeriya a shekarar 1993, Alhaji Bashir Tofa ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya kamar yadda daya daga cikin ‘ya’yansa ta sanar a sanyin safiyar wannan Litinin.

Alhaji Bashir Tofa
Alhaji Bashir Tofa © Daily Post
Talla

Kwanaki uku da suka gabata, an yi ta yada labaran karya a shafukan sada zumunta game da rauswarsa, amma daya daga cikin  ‘ya’yansa mata ta fito ta karya labarin a wancan lokaci.

Za a ci gaba da tuna Tofa da gudunmawar da yake bayarwa wajen bada shawarwari domin ci gaban Najeriya da kuma yadda za a magance matsalolin da siuka yi mata dabaibayi.

Tofa ya tsaya takarar shugaban kasa  karkashin jam’iyyar NRC , inda ya fafata da MKO Abiola na jam’iyyar SDP a zaben da masana suka bayyana a matsayin mafi inganci da aka gudanar a tarihin Najeriya.

Rahotanni sun ce, tuni aka fara shirye-shiryen gudanar da jana’izarsa a wannan safiya ta Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.