Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

Buhari ya ayyana 'yan bindigar Najeriya a matsayin 'yan ta'adda

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin murkushe ‘yan bindigar da suka addabi yankin arewa maso yammacin kasar, wadanda ya bayyana a matsayin ‘yan ta’adda.Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da kafar talabijin na Channels da ke Najeriya, inda suka tattauna akan batutuwan da suka shafi tsaro, zabe, tsarin mulki da kuma tattalin arzikin kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. © Nigeria presidency
Talla

Yayin da ya ke amsa tambayoyi akan matsalar tsaro shugaba Buhari ya bayyana cewa ya tattauna da hukumomin tsaro akan ‘yan bindigar da gwamnatinsa ta ayyana a matsayin ‘yan ta’adda kuma za su dauki matakan da suka dace wajen murkushe ta’addancin nasu.

Dangane da kiraye-kirayen da ake na kafa rundunonin ‘yan sanda masu cin gashin kansu na jihohi kuwa, shugaban Najeriya ya bayyana amincewa da matakin a matsayin hanya mara bullewa domin kuwa gwamnoni ne za su rika sarrafa jami’an tsaron bisa son ransu kamar yadda suke yi da kudade da sauran hakkokin kananan hukumomi.

Akan cece-kucen da ya biyo bayan kin sanya hannu kan sabuwar dokar zaben da shugaban ya yi Buhari ya ce a shirye ya ke ya amince da dokar amma fa bisa sharadin sai majalisun dokokin Najeriya sun yi mata kwaskwarima ta hanyar sanya ba da damar tsayar da dan takara ta hanyar maslaha, da zabin fidda gwani a kaikaice wajen tsaida dan takara a zabe, sabanin tsarin zaben ‘yar tinke ko kato bayan kato da sabuwar dokar ta dauka a matsayin zabi daya tilo na gudanar da zaben fidda gwani a tsakanin jam’iyyun siyasa.

Shugaban Najeriyar ya kuma bayyana rashin jin dadinsa akan matsalar karancin lantarkin da ake cigaba da fuskanta a Najeriya duk da kokarin da ya ce gwamnatinsa na yi wajen samarwa ‘yan Najeriya ababen morewa rayuwa da suka hada da Lantarkin,  tituna, da kuma layukan dogo.

A fannin samar da guraben ayyukan yi kuma, Buhari ya shawarci matasa ne da su yi amfani da ilimi da wayewar da suka samu wajen kirkira ko bunkasa hanyoyin dogaro da kai, amma ba daukar shaidun su na samun ilimi a matsayin tikitin dogaro kacokan akan gwamnati ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.