An samu mutane da suka harbu da cutar Korona a jihohin Najeriya
A Najeriya, alkaluman baya-bayan nan da hukumar NCDC ta fitar a yau asabar ya nuna cewa an samu sabbin bullar cutar Korona a jihohi takwas na tarayyar kasar har da babban birnin tarayya Abuja (FCT).
Wallafawa ranar:
Minti 1
Talla
Sabbin wadanda ke dauke da cutar a Najeriya sun kai 250,361, yayin da adadin wadanda suka mutu ya kai 3,092.
Bayanan raguwar adadin cutar da aka samu daga sama da 25,000 daga 13 ga watan janairun 2022 zuwa 23,768 ranar Juma'a data gabata.
Cibiyar ta kuma bayyana cewa an samu nasarar yi wa mutane 223,495 jinya tare da sallamar su a Najeriyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu