Isa ga babban shafi
Wasanni

Jose Peseiro bai raka 'yan wasan Najeriya zuwa Kamaru ba - NFF

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta ce sabon kocin da ta sanar da dauka Jose Peseiro, bai rattaba hannu a kan yarjejeniyar karbar ragamar horas da tawagar kwallon kafar kasar ba bayan kammala gasar cin kofin Afrika ta 2021 da ke gudana a Kamaru.

Super Eagles kungiyar kwallon kafar Najeriya
Super Eagles kungiyar kwallon kafar Najeriya © NFF
Talla

Augustine Eguavoen, wanda a halin yanzu ke rikon kwaryar horas da ‘yan wasan Najeriya na Super Eagles, shi ne ya jagoranci tawagar ‘yan wasan zuwa Kamaru, bayan da NFF ta kori Gernot Rohr, kasa da wata guda kafin fara gasar ta bana.

Super Eagles na Najeriya sun yi sakaci Saliyo ta farke kwallaye 4 da suka saka musu a raga.
Super Eagles na Najeriya sun yi sakaci Saliyo ta farke kwallaye 4 da suka saka musu a raga. JAVIER SORIANO / AFP

A halin da ake ciki kuma tuni Eguavoen ya jagoranci Super Eagles wajen samun nasara sau uku a jere a gasar AFCON, duk da cewa ya kwashe makonni biyu ne kawai yana horar da kungiyar kafin tafiyar gasar.

Tambarin hukumar kwallon kafar Najeriya (NFF)
Tambarin hukumar kwallon kafar Najeriya (NFF) completesportsnigeria.com

Kwanaki bayan nadin Eguavoen a matsyin kocin rikon kwarya ne, hukumar kwallon Najeriya ta sanar da Peseiro dan kasar Portugal a matsayin wanda zai karbi jagorancin ‘yan wasan Najeriya bayan kammala gasar AFCON a Kamaru.

Ana sa ran Jose Peseiro mai shekaru 61 zai kasance a Kamaru a matsayin dan kallo kafin ya karbi ragamar jagorantar Najeriya don zuwa wasannin neman tikitin gasar cin kofin duniya a watan Maris, amma bai yi balaguro ba.

Wani Jami’i da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa kafar labaran wasanni ta ESPN cewa, abinda suke bukata a yanzu shi ne farantawa ‘yan Najeriya da kuma kiyaye abinda suke so.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.