Isa ga babban shafi
Najeriya-Atiku

Uwargidar Atiku ta tsere daga kasar bisa barazana ga rayuwarta

Uwargidan Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar wato Jennifer Abubakar tayi zargin cewar tana fuskantar barazanar hallaka ta daga wasu daga cikin na kusa da shi saboda rikicin sakin dake tsakanin su yanzu haka.

Atiku Abubakar da matarsa Jenifer.
Atiku Abubakar da matarsa Jenifer. © Daily Trust
Talla

Sanarwar da ta raba wa manema labarai ta ce Jennifer tana ci gaba da samun barazanar kisa daga na kusa da tsohon mataimkin shugaban kasar, wadanda ke kokarin raba ta da kadarorin da ta mallaka.

Jaridar 'Daily Trust' ta ruwaito Jennifer na cewa tana fargabar rayuwarta da na ‘yayanta, saboda yadda masu tsaron lafiyar Atiku Abubakar da suka hada da Ibro da wasu mutane suke mata barazana da kuma kiran ‘yan uwanta da kawayen ta da kuma masu mata aiki tare da binciken kadarorinta domin kwace su, baya ga sanya ido a kan wayarta tare da na kawayenta da ‘yan uwanta.

Jenifer ta ce saboda haka ne ta fice daga ofishinta na lauya, inda ta sayar da kadarorinta tare da komawa kasar waje domin kare lafiyarta.

Jennifer ta ce ita ta san bata aikata wani laifi da ya wuce bukatar saki daga Atiku Abubakar ba, kuma tana bakin cikin amfani da wannan dama wajen bayyana halin da take ciki, amma kuma ta yi haka ne saboda fargabar da take kan lafiyarta.

Ta ce domin fadakar da jama’a halin da ta samu kanta, shine ya sa tayi amfani da wannan dama domin kada ayi amfani da haka wajen bata mata suna.

Jennifer ta yi watsi da zargin cewar ta nemi saki ne saboda Atiku ya sake auro wata mata, inda ta ce a matsayinsa na Musulmi ba ta taba tambayar sa a kan matansa ba.

Uwargidar ta ce babbar matsalar da ta shiga tsakaninsu ita ce ci gaba da zaman ta a Birtaniya domin kula da ‘yayan a da kuma muradunta, a matsayinta na wadda ke bukatar amfani da matsayinta na uwa a kan ‘yayanta wadanda suka rasa kulawar iyayan su biyu lokacin da suke girma, musamman bayan rasuwar yarta da take kula da su.

Jennifer ta ce sakamakon barkewar annobar korona, ta zabi zama da ’yayanta a lokacin, kuma bisa al’adar ‘yan arewacin Najeriya, amarya ce ke daukar nauyin miji, yayin da ita ta mayar da hankali a kan ‘yayanta.

Uwargidar tace a ranar 26 ga watan Yunin bara ta bukaci Atiku Abubakar da ya sake ta saboda tabarbarewar auran su, yayin da ta shaida masa cewar zata ci gaba da taimaka masa ko da sun rabu, abin da ya sa abokansa suka yi ta kokarin shiga tsakani domin sasanta su.

Jennifer ta mika godiyar ta ga mutane irin su Peter Okocha da Sanata Ben Obi da Tunde Ayeni da Kaftin Yahaya da Sanata Ben Bruce da suka yi ta kokarin shiga tsakani domin daidaita su.

Uwargidar ta ce ko da yake Atiku bai shaida mata auran da ya sake yi ba kamar yadda al’ada da addinin Musulunci suka tanada, ta samu labarin amaryarsa tun daga lokacin da yake zawarcin ta har zuwa lokacin auran.

Jennifer ta ce ta gayyaci amaryar auran ‘danta a Dubai a shekarar 2018 ba tare da adawa da ita ba, tare da taya ta murna lokacin da ta haihu.

Uwargidar ta ce da tana bukatar kwace kadarorin Atiku da bata mayar masa da takardun kadarorin da ya mallaka a Abuja da Jos ba, tare da bai wa direba damar kwashe motocinsa da makullin gidajensa da ke Asokoro da Yola ba.

Jennifer ta ce duk da abubuwan da suka faru, tana bukatar rabuwar su cikin lumana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.