Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar wakilai za ta binciki wasu hukumomi kan sayen gurbataccen mai

Majalisar Wakilan Najeriya ta ba da umarnin gudanar da bincike kan shigar da miliyoyin litar gurbataccen man fetur cikin kasar.

Wani gidan sayar da man fetur a Najeriya.
Wani gidan sayar da man fetur a Najeriya. WILS YANICK MANIENGUI / AFP
Talla

Matakin ya biyo bayan kudirin da Hon Mohammed Tahir Monguno ya gabatar a zauren majalisar, wanda ya samu goyon bayan daukacin takwarorinsa, wadanda suka koka kan cewa da gangan aka shigar da gurbataccen man fetur din cikin Najeriya, zalika ya kuma zama dole a hukunta wadanda suka aikata laifin.

Daga cikin wadanda ake sa ran majalisar wakilan Najeriyar za ta bincika akwai kamfanin man fetur na kasar, da hukumar kula da ingancin kayayyaki ta Najeriya SON, da hukumar kwastam ta Najeriya da sauran wasu karin hukumomin.

A ranar Larabar da ta gabata, gwamnatin Najeriya ta hannun Hukumar Kula da Man Fetur na kasar ta ce akwai yiwuwar maidawa dillalan kasashen ketare gurbataccen man fetur da Najeriyar ta saya daga gare su.

Bayanai daga kungiyar dillalan man fetur a Najeriya sun nuna cewar yawan man da aka yi kiyasin gurbatacce ne sakamakon kunsar sindarin Methanol fiye da kima ya kai kusan lita  miliyan 100 da aka shigar kasar.

Ana dai kyautata zaton matakin dakatar da sayar da gurbataccen man ne yayi sanadin samun dogayen layukan ababen hawa a sassan Najeriyar, la’akari da cewar sinadarin na methanol na iya haifar da matsala ga injunan ababen hawan da suka yi amfani da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.