Isa ga babban shafi
Najeriya - Tsaro

‘Yan bindiga da ake zargi IPOP ne sun kashe ‘yan sanda uku a Enugu

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan aware ne a kudu maso gabashin Najeriya sun kashe ‘yan sanda uku tare da raunata wasu biyu.

Wasu 'yan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra.
Wasu 'yan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra. http://naijagists.com
Talla

A ranar Alhamis ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani shingen bincike na ‘yan sanda a Enugu, babban birnin jihar Enugu, kamar yadda wani babban jami’in ‘yan sandan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

“Mun rasa jami’ai uku” sannan wasu biyu kuma sun samu raunuka, in ji shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Daniel Ndukwe ya tabbatar da faruwar harin amma ya ki tabbatar da adadin wadanda suka mutu.

"Yace har yanzu bamu da cikakken bayanai da suka shafi lamarin, amma an fara farautar 'yan bindigar,"

 

A yankin Kudu maso Gabashin Najeriya dai ana fama da tashe-tashen hankula, inda a shekarar da ta gabata aka kashe 'yan sanda da wasu jami'an tsaro sama da 130, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana.

Hukumomin kasar dai sun dora alhakin kai hare-hare a kan haramtacciyar kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra a yankin ‘yan kabilar Igbo, ko kuma reshenta da ke dauke da makamai da ake kira ESN.

Kungiyar dai ta musanta alhakin wannan tashin hankalin yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.