Isa ga babban shafi
Najeriya - IPOB

An kashe ‘yan sanda hudu a yankin kudu maso gabashin Najeriya

‘Yan bindiga da ake zargin ‘yn awaren Biafra ne sun kashe ‘yan sanda 4 a mabanbantan hare-hare da suka kai a kudu maso gabashin Najeriya.

Bindigogi dake hannun 'yan ta'adda a wani yankin Najeriya.
Bindigogi dake hannun 'yan ta'adda a wani yankin Najeriya. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo
Talla

A hari na farko da ya auku a ranar Lahadi, ‘yan bindiga sun tarwatsa ofishin ‘yan sanda na garin Isu a jihar Imo, inda jami’an ‘yan sanda 2 suka mutu nan take, wani guda ya samu rauni, a cewar kakakin ‘yan sandan jihar Michael Abatam.

Ya ce ‘yan sanda sun yi fito na fito da su ‘yan bindigar da ake zargi ‘yan kungiyaar IPOB ne, lamarin da ya sa suka tsere zuwa wani otel don neman mafaka, amma jami’an suka bi bayansu, inda suka kame 17 daga cikinsu.

Hari na biyu

Zalika, hari na biyun da ya auku a ranar Lahadi, wani kwantan bauna ne da ‘yan bindigar suka yi a jihar Anambra, inda suka kashe jami’an ‘yan sanda 2 daga cikin ayarin wani babban jammi’in gwamnatin jihar.

Samun karuwar hare-hare

Yankijn kudu maso gabashin Najeriya yana fuskantar hauhawar tashin hankali, inda a shekarar da ta gabata, ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan awaren Biafra ne suka kashe sama da ‘yan sanda 130 kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka ruwaito.

Fiye da mutane miliyan daya ne suka mutu a yakin basasa da aka shafe watanni 30 ana yi, bayan da a shekarar 1967 wasu sojoji daga ‘yan kabilar Igbo suka ayyana ‘yantatar kasar Biafra.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.