Kashin farko na 'yan Najeriya dake Ukraine ya isa gida
Kashin farko na 'yan Najeriya da suka makale a Ukraine dake yaki da Rasha ya isa filin tashi da saukara jiragen saman Abuja, babban birnin kasar da safiyar wannan Juma'a.
Wallafawa ranar:
Shugabar ‘yan Najeriya mazauna ketare Abike Dabiri Erewa ta wallafa haka ta shifin twitta, tare da sanya hotunan isar ‘yan Najeriyar cikin jirgin saman Max Air samfurin VM602 a filin Namdi Azikwe dake Abuja.
Shima Shugaban kwamitin harkokin waje a Majalisar Wakilan Najeriya Yusuf Buba dake cikin jami'an gwamnatin kasar da suka je Bucharest, babban birnin Romania domin taho da 'yan Naeriyar ya tabbatar da isowar dalibai 451 zuwa gida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu