Isa ga babban shafi
Najeriya-Kebbi

'Yan bindiga sun kashe mayakan sa kai 66 a jihar Kebbi

Wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai a Najeriya sun kai hari Jihar Kebbi inda suka hallaka 'yan sakai da ke samar da tsaro a yankin 66 a yankin Sakaba.

Wasu makamai da ake kwace a hannun 'yan bindigar arewacin Najeriya.
Wasu makamai da ake kwace a hannun 'yan bindigar arewacin Najeriya. © Premium Times
Talla

Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne da misalin karfe 10 na safiyar litinin a garin Anene, inda suka dinga bi gida-gida suna kashe mutane tare da sace dukiyar su.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewar, ‘Yan bindigar sun kutsa kai ne garin haye akan babura kamar yadda aka saba, inda suka kwashe kusan sa’oi 10 suna aika aika kafin barin garin.

Mazaunin garin wanda yace harin ya ritsa da shi a gida, ya bayyana cewar bayan mutane 66 da ‘Yan bindigar suka kashe, sun kuma jikkata wasu da dama, tare da kora dabbobin su da suka hada da kaji da awaki da kuma shanu.

Kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi Nafiu Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya danganta shi da wata arangamar da akayi tsakanin Yan Sakan da Yan bindigar.

Abubakar ya ce lokacin da ‘yan bindigar ke tserewa hare haren da jami’an tsaro ke kai musu a Jihar Neja sun ci karo da Yan Sakan wadanda suka afka musu, abinda ya sa suka kai harin daukar fansa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da kisan wanda ya bayyana shi a matsayin abin takaici, yayin da ya bukaci jami’an tsaro da su kara kaimi wajen dakile ayyukan Yan ta’addan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.