Isa ga babban shafi
Najeriya - Tallafin man fetur

Najeriya ta ce dole ne ta cire tallafin mai kamar yadda ta cire na lantarki

Gwmnatin tarayyar Najeriya ta ce  ta yi nasarar janye tallafin wutar lantarki ba tare da an sani ba, kuma janye tallafin man fetur ne abin da za ta yi nan gaba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. businessday
Talla

Ministar kudi da tsare tsaren kasa ta kasar, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a wani taron ministocin kudi na kasashen Afrika da asusun bada lamuni na duniya.

Ahmed ta ce annobar Covid-19 da kuma babban zaben kasar mai zuwa ne ma ya kawo cikas a game da janye tallafin mai.

Ministar ta ce tallafin man fetur ne ya zame wa gwamnatin Najeriya babbar matsala, inda ta kara da cewa tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya zai tsananta al’amura.

Ta bayyana fatan samun amincewar majalisar dokokin kasar don ci gaba da shirin gwamnati na janye tallafin man fetur gaba daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.