Isa ga babban shafi
Najeriya-siyasa

Gwamnatin Najeriya ta ce jami'anta da ke takara ba za su sauka daga mukamansu ba

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce za ta yi amfani da dokar zabe ta sherkarar 2022, amma fa za ta cire  sashe na 84, karamin sashe na 12 wanda ya ce dole ne duk wani mai rike da mukamin gwamnati da ke da sha’awar yin takara a zaben kasar ya sauka daga mukaminsa.

Ministan shariá na Najeriya Abubakar Malami
Ministan shariá na Najeriya Abubakar Malami Daily Post
Talla

Wani kakakin a’aikatar shari’a ta kasar, Dokta Umar Gwandu ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a.

Wannan sanarwar  na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da wata kotu da ke zamanta a garin Umahia ta jihar Abia a kudu maso gabashin kasar ta umurci ministan shari’a na kasar, Abubakar Malami da ya cire sashen ba tare da bata lokaci ba.

Gwandu ya ce matakin da ma’aikatar shariar ta dauka, biyayya ce ga umarnin da kotu ta bayar a Juma’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.