El-Rufa'i ya ziyarci fasinjojin da harin jirgi ya rutsa da su
Gwamnan Jihar Kaduna da ke Najeriya Malam Nasir El Rufai ya ziyarci wasu daga cikin fasinjojin da suka samu raunuka sakamakon harin da ‘Yan bindiga suka kai akan jirgin kasa akan hanyar Kaduna zuwa Abuja a yammacin jiya..
Wallafawa ranar:
Gwamnan wanda ya samu rakiyar wasu daga cikin jami’an gwamnatinsa ya jajanta wa wadanda suka samu raunukan a asibitin soji dake Kaduna, cikin su harda tsohon mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Ibrahim Wakalla Mohammed.
El Rufai ya yaba wa jami’an agajin gaggawa tare da jami’an tsaro saboda rawar da suka taka wajen kai dauki ga mutanen da hadarin ya ritsa da su, yayin da aka kai wadanda suka samu raunuka asibiti domin kula da lafiyarsu.
Gwamnan ya yi alkawarin daukar nauyin kudin jinyar duk wadanda hadarin ya ritsa da su.
Wani daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya lokacin harin, ya shaidawa RFI Hausa cewar akalla mutane 7 suka mutu a harin sakamakon harbi da bindiga, yayin da ‘Yan bindigar suka kwashe wasu fasinjojin suka gudu da su.
Daga cikin wadanda aka tabbatar da mutuwar su harda wata likita, Dr. MiChinelo Megafu dake aiki a asibitin St Geralds da ke Kaduna.
Shi ma shugaban rundunar sojin kasa Laftanar Janar Farouk Yahya, yau ya ziyarci inda aka kaiwa jirgin hari tare da jami’ansa, inda ya bada umurnin farautar 'Yan bindigar domin ceto wadanda aka gudu da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu