‘Yan ta’adda sun kashe dakarun Najeriya 11 tsakanin Kaduna zuwa Birnin Gwari
Akalla dakarun Najeriya 11 ne ‘yan ta’adda suka kashe bayan kwantaon bauna da suka yi musu a babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, hanyar da aka yi ittifakin tana daya daga cikin hanyoyi mafi hadari a yankin arewacin Najeriya.
Wallafawa ranar:
Majiyoyin tsaro sun ce daruruwan ‘yan ta’addan sun yi wa sojojin kwanton bauna ne, inda har ma suka kona motoci masu sulke biyu a ranar Lahadi.
Majiyoyin sun ce bayan dakarun Najeriya sun hango ‘yan ta’addan da dimbim shanu ne suka yanke shawarar tinkarar su, bisa zargin cewa fashin su suka yi, amma aka yi rashin sa’a ba su ankare cewa ‘yan ta’addan na da yawa ba.
Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito wani mazaunin yankin na cewa da safiyar Litinin ne aka aike da wasu dakaru masu damara yankin don kwashe gawarwakin sojojin da aka kashe, yana mai cewa sai da shi da kansa ya kirga gawarwakin sojoji 11 da aka zuba a bayan akori kura.LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu