Isa ga babban shafi

Osinbajo ya bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo.
Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo. REUTERS
Talla

Osinbajo ya bayyana takarar tasa ce a sakon da ya wallafa shafinsa na Twitter.

A cikin sanarwar tasa, Osinbajo ya wasa kansa da cewar ya s hafe shekaru 7 da suka gabata yana jagorantar Najeriya tare da shugaban kasar Muhammadu Buhari, inda suke fuskantar kalubale iri-iri da su ne mafiya sarkakiya a tarihin kasar,  to amma hakan ba zai hana su cigaba da aiwatar da aniyarsu ta tabbatar da tsaro, bunkasa tattalin arziki da kuma samar da ababen more rayuwa ga ‘yan Najeriya ba.

Osinbajo ya cigaba da cewa, ya ziyarci zaratan sojojin Najeriya da ke yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas da sauran fararen fula da ke sansanonin ‘yan gudun hijira, inda ya taya su jimamin halin da suke ciki.

Kafin bayyana aniyar ta sa dai, sai da Farfesan ya fara ganawa da wasu gwamnonin jam'iyyarsu ta APC a karshen mako.

Mataimakin shugaban Najeriyar shi ne na baya bayan nan da ya bayyana aniyar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa, baya ga ministan Sufuri Rotimi Ameachi da ya fito daga yankin kudu maso kudancin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.