Isa ga babban shafi
Sokoto

Hatsarin kwale-kwale ya kashe mutane 26 a Sokoto

Akalla mutane 26 suka mutu a Jihar Sokoto dake Najeriya sakamakon hadarin kwale kwale a kogin Shagari da ke Jihar.

Ana yawan samun hatsarin jiragen ruwa a Najeriya.
Ana yawan samun hatsarin jiragen ruwa a Najeriya. REUTERS/Darren Whiteside
Talla

Wani jami’in Mulki a Yankin Aliyu Dantani wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce daga cikin wadanda suka mutu akwai mata 21 da yara kanana guda 5, kuma tuni aka ciro gawarwakin su.

Dantani ya ce basu iya tantance yawan mutanen dake cikin kwale kwalen lokacin da aka samu hadarin ba, ko kuma dalilin da ya haifar da hadarin.

A watan jiya mutane 13 suka nitse a ruwa lokacin da suke tserewa hare haren Yan ta’adda a Jihar Neja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.