Isa ga babban shafi

Rashawa ce ta hana sojin Najeriya aiki - Amurka

Kasar Amurka ta ce cin hanci da rashawa da rashin hukunci daga bangaren shari’a na daga cikin matsalolin da suka haifar da kama-karya a tsakanin jami’an soji da ‘Yan sanda da kuma ‘Yan Sandan farin kaya dake aiki a Najeriya, abinda ke hana su gudanar da ayyukansu kamar yadda aka saba.

Shugaba Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo na nada Manjo Janar Faruk Yahaya a matsayin sabon Hafsan sojin kasar
Shugaba Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo na nada Manjo Janar Faruk Yahaya a matsayin sabon Hafsan sojin kasar © Nigeria presidency
Talla

Wani rahotan da gwamnatin Amurka ta gabatar wanda ya mayar da hankali akan taken hakkin Bil Adama a shekarar 2021, ya duba batutuwa da dama da suka hada da dangantaka tsakanin hukumomin da fararen hula da kare hakkin Bil Adama da cin hanci da rashawa a hukumomin gwamnati da da dama da kuma kama karyar da ake samu a tsakanin jami’an tsaro.

Amurka ta bayyana cewar cin hanci da rashawa tsakanin jami’an gwamnati da kuma bangaren shari’a ya haifar da kama karya a cikin kasar, kuma ya zama babbar kalubale a tsakanin jami’an tsaro, musamman ‘Yan Sanda da soji da kuma ‘Yan Sandan farin kaya.

Rahotan ya ce duk da yake ‘Yan Sandan da soji da kuma ‘Yan Sandan farin kayan na da shugabannin fararen hula, lokaci zuwa lokaci suna yin gaban kan su wajen gudanar da wasu ayyukan da suka saba ka’ida ba tare da sanin magabatan su ba.

Amurka tace wadanann jami’ai kan yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar lumana da kuma kama wadanda ake zargi da aikata laifuffuka, yayin da ta zargi ‘Yan Sanda da amfani da karfin da ya wuce kima wajen gudanar da irin wadannan ayyukan nasu.

Rahotan yace take hakkin Bil Adama da cin hanci da rashawa da kashe mutane ba bisa ka’ida ba na ci gaba da zama abin damuwa a kasar, sakamakon rahotannin da ake samu dangane da karuwar matsalar daga ‘Yan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.