Isa ga babban shafi

Ortom ya bayyana dalilan da za su hana kabilar Idoma mukamin Gwamna

Gwamnan Jihar Benue da ke Najeriya Samuel Ortom ya bayyana dalilin da zai hana baiwa ‘yan kabilar Idoma damar zama Gwamna a Jihar a zaben shekara mai zuwa, sabin alkawarin da yayi a shekarun baya cewar a shirye yake ya ga sun karbi mulki a karon farko.

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom.
Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom. © Twitter/@GovSamuelOrtom
Talla

Daga cikin dalilan da Ortom ya gabatar a matsayin abinda zai hana Idoma zama gwamna a Benue harda da rashin hadin kai a tsakanin kananan hukumomi guda 9 dake ke Yankin su da kuma rashin amincewa a tsakanin manyan jam’iyyun jihar na daukar matsayin baiwa yankin takarar gwamna a shekara mai zuwa.

Gwamnan ya shaidawa Jaridar Premium Times cewar idan yanzu jam’iyyar sa ta PDP ta tsaida ‘dan takara daga Yankin Idoma, yayin da APC ta tsayar daga Yankin Tibi, APC zata samu nasara domin Yankin Tibi ke da kahsi biyu bisa 3 na al’ummar Jihar, saboda haka ya dace jam’iyyun gaba daya su yanke hukuncin tsayar da takara daga yankin kafin a cimma nasarar samun gwamna daga wancan bangaren.

Tun da aka dawo da mulkin dimokiradiya a shekarar 1999 Yan kabilar Tibi ne ke zama Gwamnan Jihar Benue, yayin da Yan kabilar Idoma ke zama mataimaka.

Duk wani yunkuri na ganin kujerar gwamnan jihar ya koma bangaren Idoma yaci tura saboda yadda jama’ar Tibi suka mamaye kasha biyu bisa 3 na al’ummar jihar baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.