Isa ga babban shafi
Najeriya-Birtaniya-IPOB

Birtaniya ta amince da sanya IPOB a jerin kungiyoyin 'yan ta'adda

Gwamnatin Birtaniya ta sauya matsayinta a kan kungiyar nan mai fafutukar neman kasar Biafra wato IPOB, tana mai amincewa da saka ta a jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda da gwamnatin Najeriya ta yi.

 Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB wanda yake tsare a hannun gwamnatin Najeriya tun a watan Yulin shekarar 2021.
Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB wanda yake tsare a hannun gwamnatin Najeriya tun a watan Yulin shekarar 2021. AFP - STEFAN HEUNIS
Talla

A daftarin manufarta ta bayar da mafaka da ta sabanta a watan Mayun nan, gwamnatin Birtaniya ta cire ‘yayan kungiyar IPOB daga cikin masu neman mafaka a Ingila.

A cikin watan Afrilun shekarar 2021 ne rahotanni suka bayyana a kafafen yada labarai cewa, Birtaniya na shirin bada mafaka ga ‘yayan kungiyar ‘yan awaren IPOB da ake musguna wa, a matsayin wani bangare na manufofinta a kan ‘yan gudun hijira da ta walllafa a lokacin.

Amma ‘yan kwanaki bayan wallafa daftarin, gwammanti Birtaniya ta soke shi, biyo bayan korafi daga takwararta ta Najeriya.

A cikin daftarin manufofin nata, gwamnatin Birtaniya ta bayyana IPOB a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda, wadda za ta cire ta daga shirinta na bada mafaka, sakamakon hannu da take da shi a kashe kashe da tashin hankali a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Daftarin manufofin ya kuma ce, duk wanda aka cire daga jerin wadanda suka cancanci mafaka, tabbaci hakika ba ya cikin wadanda za su samu kariya ta jinkai.

‘Ya bindiga da ake zaton ‘yayan kungiyar IPOB ne, sun tsananta aikata ta’asa a yankin kudu maso gabashin Najeriya a baya bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.