Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kashe Janar da sojoji 7 a Taraba

Ana fargabar wasu ‘Yan bindiga a Jihar Taraba da ke Najeriya da kashe kwamandan sojin Bataliya ta 93 dake Takum mai rike da mukamin Birgediya Janar tare da wasu sojojin sa guda 7.

Alamun 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a Najeriya
Alamun 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a Najeriya Daily Trust
Talla

Jaridar Leadership da ake wallafawa a Najeriya ta tabbatar da kai harin daga bakin shugaban karamar Hukumar Takum Hon Shiban Tikari, amma bai yi karin haske akan yadda lamarin ya auku ba.

Tikari ya ce yanzu haka shi da wasu jami’an tsaro na jeji inda suke kokarin gano gawarwakin sauran sojojin dake tawagar Kwamandan da suka bata.

Jaridar ta ruwaito shaidar gani da ido na cewa an samu aukuwar lamarin ne tsakanin Takum zuwa kauyen  Tanti akan hanyar zuwa Jalingo.

Majiyar ta ce Kwamandan na kan hanyar zuwa Jalingo ne lokacin da Yan bindigar suka yi wa tawagarsa kwantan bauna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.