Isa ga babban shafi

Ina tare da Tinubu dari bisa dari a zaben 2023 - El Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa’i ya fito fili wajen bayyana goyon bayansa ga takarar neman kujerar shugabancin Najeriya da tsohon gwamnan Legas Ahmed Bola Tinubu ke yi a karkashin jam’iyyarsu ta APC.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad el-Rufai.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad el-Rufai. © Daily Trust
Talla

El Rufa’i ya bayyana haka ne bayan karbar bakuncin Tinubu tare da mukarrabansa da suka hada da tsohon gwamnan Borno Kashim Shettima da kuma tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu.

Manyan bakin tare da gwamnan jihar at Kaduna sun yi wa Tinubu rakiya zuwa babban filin wasa na Murtala da ke garin Kaduna, inda suka gudanar da gangamin neman goyon bayan wakilan jam’iyyar APC da za su kada kuri’a a zaben fidda gwani tsakanin wadanda ke neman a tsayar da su takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Jagoran Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Bola Tinubu.
Jagoran Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Bola Tinubu. STEFAN HEUNIS / AFP

Tsohon gwamnan Legas Bola Tinubu dai na daga cikin fitattun ‘yan jam’iyyar APC na gaba gaba da ake ganin suna da damar samun tikitin tsaya mata takarar kujerar shugaban kasa domin maye gurbin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Daya daga cikin masu takarar da ake ganin ka iya zama kalubale babba ga Tinubu shi ne mataimakin shugaban kasa mai ci Farfesa Yemi Osinbajo, wanda shi ma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara zaben shugabancin Najeriya da ke tafe.

Sai dai a cikin watan Afrilu, Tinubu ya ce ko gezau baya yi dangane da tsayawa takarar Osinbajo ba, kamar yadda wasu ke tunani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.