Isa ga babban shafi
Zaben Najeriya

Dole shugabancin Najeriya ya koma kudu - gwamnonin arewa

Gwamnonin Jam’iyyar APC da suka fito daga yankin arewacin Najeriya sun ce, babu abin da ya sauya dangane da matsayinsu na ganin ‘dan takarar zaben shugaban kasar shekara mai zuwa ya fito daga yankin kudancin kasar.

Jiga jigan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
Jiga jigan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya © Femi Adesina
Talla

Bayan ganawar da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau, shugaban gwamnonin arewa Simon Lalong ya ce har yanzu suna kan bakarsu ta ganin an tabbatar da adalci wajen raba mukaman siyasar kasar da kuma dorewar karba-karba.

Lalong ya ce gwamnonin APCn 13 sun amince da wannan shiri saboda dorewar zaman lafiya da kuma yin adalci ga kowanne bangare, yayin da gwamnan Kogi Yahya Bello yaki amincewa da matakin.

Shugaban gwamnonin arewacin kasar ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba su umurnin ganawa da 'yan majalisar zartarwar jam’iyyar APC domin daukar matsayin bai-daya kafin fara taron.

Sai dai wasu rahotanni na bayyana cewar, shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya shaida wa ‘yan majalisar zartarwar jam’iyyar cewar Sanata Ahmed Lawal, shugaban majalisar dattawa shi ne suka amince da shi a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Ya zuwa yanzu dai babu wani tabbaci daga shugabannin jam’iyyar dangane da daukar wannan matsayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.