Isa ga babban shafi

Najeriya na shirin dakile 'yancin 'yan kasar - MRA

Kungiyar Kare Aikin Jarida ta MRA ta bukaci gwwmnatin tarayyar Najeriya da ta dakatar da yunkurinta na samar da dokar sanya ido kan shafukan sada zumunta.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya bada umarnin kafa dokar
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya bada umarnin kafa dokar © Nigeria presidency
Talla

Kungiyar ta MRA ta bayyana kudirin dokar aikace-aikacen da Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta NITDA ta zayyana a matsayin wani yunkuri na kwace dukkanin nau’ukun iko daga Majalisar  Tarayyar kasar tare kuma da keta hakkokin ‘yan Najeriya.

Shugabar Hukumar ta NITDA, Hadiza Umar ta ce, shugban kasar Mu. Buhari ne ya bada umarnin samar da dokar domin kula da duk wani aikin sadarwar zamani a Najeriya.

Shugaban Kungiyar Kare AIkin Jarida ta MRA, Mista Ayode Longe ya ce, gwanmnatin tarayyar Najeriya na kokarin bullowa ta bayan-fage ba tare da ratsawa ta Majalisar Dokoki ba domin cimma boyayyen burinta na dakile ayyukan shafukan sada zumunta.

Duk da cewa, gwamnatin ba ta ambaci shafukan sada zumunta karara ba, amma kungiyar ta MRA ta ce, makasudin gwamnatin shi ne sanya ido kan shafukan ta hanyar tilasta musu yin rajista, inda daga nan kuma za ta fara dakile ‘yancin fadan albarkacin baki.

MRA ta ce, yunkurin gwamnatin tarayyar ya saba wa ayar doka ta 19 da ke kunshe a cikin kundin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.