Najeriya da Birtaniya sun sanya hannu a yarjejeniyar dakile kwararar baki
Najeriya da Birtaniya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar dakile kwararar bakin-haure, wadda a karkashin ta za a rika mayar da wadanda suka tsallaka zuwa kasar Turan ba bisa ka’ida ba, da kuma sauran masu aikata laifuka zuwa gida Najeriya.
Wallafawa ranar:
Tuni dai kashin farko na bakin-hauren da aka kora daga Birtaniya suka bar kasar zuwa Najeriya da Ghana, inda a ranar 30 ga watan Yuni, aka iza keyar ‘yan Najeriya 13 zuwa birnin Legas, sai kuma ‘yan Ghana 8, da suka hada da bakin-haure 5 da masu aikata laifuka 3.
Wata sanarwar ofishin harkokin cikin gidan Birtaniya ta ce an yankewa dukkanin masu laifin da aka kora daga Birtaniya hukuncin daurin shekaru sama da 64 a gidan Yari, idan aka hadasu waje guda.
Daya daga cikin manyan jami’an gwamnatin Birtaniya, ya kara da cewar, a halin da ake ciki an iza keyar mutane sama da 10,000 daga Birtaniyar zuwa kasashensu a tsakanin watan Janairun shekara ta 2019 zuwa Mayu na shekarar 2022.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu