Isa ga babban shafi

Najeriya: Ambaliyar ruwa ta wuce da wata mota da fasinjojinta a Legas

A Legas da ke kudu maso yamacin Najeriya, wata mummunar ambaliyar ruwa ta daga hankalin mazauna wasu yankunan birnin, inda har ta yi awon gaba da wata mota da fasinjojin da ke cikinta zuwa wata magudanar ruwa a unguwar Orile-Agege.

Birnin Lagos a Najeriya na fuskantar ambaliyar ruwa duk shekara.
Birnin Lagos a Najeriya na fuskantar ambaliyar ruwa duk shekara. © guardian.ng
Talla

Wasu  mutane 2 mazauna unguwar sun bata, inda yanzu haka ake nemansu.

Masu aikin ceto daga hukumr agajin gaggawa ta jihar Legas, da kuma ta kasa da ma  na hukumaar kwana kwana ta jihar Legas suna aikin lalubo wadanda suka bace.

Jami’in hulda da jama’a  na hukumar bada agajin gaggawa ta kasar, Ibrahim Farinloye,  ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa jami’ansu na can suna aikin ceto.

Lamarin ya auku ne a kusa da mashigin ruwa na Kirikiri da misalin karfe 7 da minti 45 na daren Juma’a, amma sai a Asabar din nan aka samu labarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.