Isa ga babban shafi

'Yan Najeriya na cikin hadarin kamuwa da cutar Marburg

Cibiyar Kula da Cutuka Masu Yaduwa a Najeriya ta ce kasar na fuskantar hadarin samun bullar kwayar cutar  Marburg  mai alaka da Ebola, iirn wadda aka samu a kasar Ghana.

Cutar Marburg na dauke da irn alamomin cutar Ebola
Cutar Marburg na dauke da irn alamomin cutar Ebola © CDC/ Dr. Frederick Murphy
Talla

A wata sanarwa a Larabar nan, daraktan  cibiyar, Dokta Ifedayo Adetiba ya ce, an gano cewa cutar na iya shigowa Najeriya ce bayan bincike da suka gudanar a kan bullarta a Ghana.

Cutar Marburg tana zuwa ne da zazzabi mai tsanani a jikin dan adam kamar yadda cutar Ebola take yi.

Dokta Adetifa ya ce, bisa alkalumman da aka samu, tasirin shigowar  cutar a kan al’ummar Najeriya matsakaici ne, la’akari da nazarin da cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta yi, duba da nisan Ghana zuwa Najeriya, da kuma irin binciken da hukumomi ke yi kafin su bari baki su shiga kasar.

Adetifa ya ce, a halin da ake ciki, babu wanda ya harbu da wannan cuta ta Marburg a Najeriya, inda ya kara da cewa ana daukar matakan hana cutar shigowa Najeriya.

Bullar cutar Marburg a Ghana ita ce, karo na biyu a nahiyar yammacin Afrika, bayan kasar Guinea da aka samu bullarta a shekarar 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.