Isa ga babban shafi

Buhari na shirin balaguro zuwa Liberia gobe

Shugaban Najeriya Muhammaddu Buhari na shirin balaguro zuwa Liberia, inda zai gabatar da jawabi kan matsalar tasaro a yankin Yammacin Afrika da gudanar da sahihin zabe da kuma mutunta doka.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

Buharin zai hadu da wasu takwarorinsa na kasashen Afrika a birnin Monrovia a daidai lokacin da kasar ta Liberia ke bikin cika shekaru 175 da samun ‘yancin kai daga masu mulkin mallaka.

A gobe Talata ne dai, shugaban zai kama hanyar zuwa kasar ta Liberia kamar yadda sanarwar da mai taimaka masa kan yada labarai, Garba Shehu ya fitar ta bayyana.

Wannan na zuwa ne akalla kwanaki biyu da ‘yan ta’adda suka saki wani faifai bidiyo da ke nuna yadda suke azabtar da fasinjojin jirgin kasan da suka yi garkuwa da su akan hanyar Abuja-Kaduna.

A cikin bidiyon dai, ‘yan ta’addar sun yi barazanar sace shugaba Buhari tare da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.