Isa ga babban shafi

Rundunar Hadin kai ta kashe 'yan ta'adda 60 tare da ceto 'yan matan Chibok 3

Rundunar Hadin kai dake yaki da 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabashin Najeriya sun samu nasarar kashe yan ta'adda 60 tare da kama 120 a wasu samame da suka kai maboyar yan ta'addar a cewar kwamandan runduna Janar  Christopher Musa.

Wasu daga cikin daliban makarantar sakandiren Chibok kenan, da Boko Haram suka sace a shekarar 2014
Wasu daga cikin daliban makarantar sakandiren Chibok kenan, da Boko Haram suka sace a shekarar 2014 © The Guardian Nigeria
Talla

Kwamandan rundunar hadin kai Janra Christopher Musa yayin taron manema labarai a Maiduguri a jiya juma'a ya na mai bayyana cewa rundunar tar da hadin gwuiwar sauren rudunoni na kokarin ganin ta toshe hanyoyin da yan ta'addar ke amfani da su wajen cimaka da abinci da wasu ababe daban.

Wannan kokarin rundunar hadin kai ya taimaka matuka wajen kama wasu daga cikin masu aiki da kungiyoyin yan ta'addan,irin su  Haruna Fulani da Umaru ranar 13 ga watan Yuli,mutanen da ke taimakawa kungiyoyin yan ta'addan.

Babban jami'in runduhnar Hadin kai ya bayyana cewa daga cikin kayakin da suka kama vsun hada da takalman mata ,nikab,auduga da sauren su.Janar din ya bayyana cewa daga ranar 27 ga watabn yuni zuwa 25 ga watan Yuli,dakarun sun yi nasar ceto 'yan matan Sakandary na Chibok uku da suka hada da Ruth Bitrus, Karuna Luka dake dauke da yaro daya sai  Hannatu Musa mai dauke da ya'a guda biyu.

A shekara ta 2014 ne yan kungiyar Boko Haram  suka yi awon gaba da dalibai 276 masu shekaru kama daga  16 zuwa 18 a makarantar sakandary ta Chibok.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.