Isa ga babban shafi

Fargabar ta'addanci ta tilasta tsaurara tsaro a gidajen yarin Zamfara Kebbi da Katsina

Mahukuntan Najeriya sun jibge tarin jami’an tsaro a yankunan da gidajen yarin jihohin Katsina Kebbi da kuma Zamfara su ke, a wani yunkuri na dakile duk wata barazana harin ta’addanci.

Jami'an DSS a Najeriya.
Jami'an DSS a Najeriya. guardian.ng
Talla

Wasu dai na alakanta jibge wadanda jami’ai da kokarin kaucewa irin matsalar fasa gidan yarin da Najeriyar ta fuskanta a gidan yarin Kuje da ke Abuja fadar gwamnatin kasar.

Shaidun gani da ido sun ruwaito yadda jami’an tsaron da aka jibge rike da manyan makamai ke ci gaba da sintiri a yankunan gidajen yarin jihohin 3.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki 11 bayan jaridar Premium Times ta wallafa rahoton gargadin sashen bayanan sirri na Sojin kasar da ke bayyana yiwuwar harin ta’addanci a gidajen yarin jihohin arewacin kasar 3.

A jihar Katsina kakakin gidan yarin jihar Najib Idris ya tabbatarwa jaridar ta Premium Times cewa matakin jibge jami’an tsaron na da nufin bayar da kariya a gidan yarin don kaucewa harin ta’addancin.

Ba kadai a kewayen gidan yarin ba, hatta a tsakar jihar Katsina an ga karuwar zirga-zirgar jami’an tsaro a yankunan da suka kunshi Unguwar Yari da Kofar Soro da kuma sabon gidan yarin da ke kan titin zuwa Jibia duk da kasancewarsa gab da barikin Soji.

A jihar Kebbi rahotanni sun ce haka abin ya ke ta yadda jami’an tsaro suka yi dandazo a yankin Illelar Yari yayinda ake tsananta bincike kan duk masu shige da fice a anguwar.

Haka zalika jihar Zamfara inda al’ummar yankin Unguwaer Gwaza da ke Gusau ke ganin karuwar zirga-zirgar jami’an tsaro baya ga was una daban da aka jibge a kofar gidan yarin da ke wajen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.