Isa ga babban shafi

An kara sako fasinjojin jirgin kasa a Najeriya

An sako hudu daga cikin yaran da aka yi garkuwa da su a cikin jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris.

Karin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da aka sako su a yau Laraba tare da Tukur Mamu da ke shifa tsakani da kuma Sheikh Ahmad Gumi
Karin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da aka sako su a yau Laraba tare da Tukur Mamu da ke shifa tsakani da kuma Sheikh Ahmad Gumi © daily trust
Talla

An sace yaran ne tare da iyayensu da sauran fasinjoji a lokacin da ‘yan ta’adda suka jefa bama-bamai a kan titin jirgin tare da harbe wasu mutane.

An saki mutanen a mabanbantan lokuta, yayin da suka yi tsawon watanni hudu a hannun mayakan.

A wata sanarwa da ya fitar, Tukur Mamu, mawallafin da ke zaune a Kaduna, wanda ya shiga tsakani a sakin wasu fasinjojin, ya ce an sako yaran da iyayensu ne bayan da Sheik Ahmad Gumi ya shiga tsakani.

Mahaifin yaran hudu ma'aikaci ne a Hukumar Majalisar Dokokin kasar.

Kamar yadda rahotanni daga kaar suka bayyana, babu wani shiga tsakani da Hukumar ko majalisar dokokin kasar ta yi a madadinsa tun lokacin da aka kai harin.

Daga cikin mutum shida da mayakan suka sako, akwai Abubakar Idris Garba, wanda shine mahaifin ‘ya’yan hudu, da matarsa Maryama Abubakar Bobbo da babban dansu, Ibrahim Abubakar Garba mai shekaru 10.

Sauran sun hada da Fatima Abubakar Garba ’yar shekara 7, Imran Abubakar Garba dan shekara 5 sai kuma Zainab Abubakar Garba mai shekara daya da rabi kacal.

Abubakar da ne ga Manjo Janar Idris Garba mai ritaya, wato Janar Garba wanda yanzu ke fama da rashin lafiya, kuma dan asalin jihar Neja wanda ya kasance tsohon shugaban mulkin soja na jihohin Kano da Benue a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasar, Janar Ibrahim Babangida.

Garba ya roki gwamnatin kasar, lokacin da wannan al'amari ya faru da ta shiga tsakani wajen sako yaronsa, surukarsa da kuma jikokinsa.

Latsa alamar sauti domin asuraron rahoton Aminu Sani Sado daga Kadunan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.