Isa ga babban shafi

Kusan mutum 50 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Jigawa da ke Najeriya

Gwamnatin Jihar Jigawa dake arewacin Najeriya tace akalla mutane 50 suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon mummunar ambaliyar da aka samu a sasan jihar.

Gwamnan jihar kenan, Jigawa Alhaji Badaru Abubakar
Gwamnan jihar kenan, Jigawa Alhaji Badaru Abubakar jigawastate.gov.ng
Talla

Shugaban hukumar agajin gaggawa a Jihar, Sani Yusuf ya shaidawa manema labarai cewar bayan mutuwar da aka samu, ambaliyar ta kuma rusa dubban gidaje, abinda ya kaiga tilastawa wasu mutane samun mafaka a gine ginen gwamnati.

Yusuf yace gwamnatin jihar ta samar da sansanonin wucin gadi guda 11 domin kula da wadanda ambaliyar ta shafa, cikin su harda mutanen kauyan Balangu, inda ruwan ya rusa gidaje 237, ya kuma kashe mutane 4.

Jihohin arewacin Najeriya da dama na fuskantar matsalar ambaliya saboda ruwan saman da ake ci gaba da shararawa.

Cikin jihohin da aka samu ambaliyar harda Borno da Yobe da Jigawa da kuma Gombe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.