Isa ga babban shafi

Buhari bai shirya mulkin Najeriya ba - Baba Ahmed

Kakakin Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya, Hakeem Baba Ahmed ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai shirya yadda zai mulkin kasar ba duk da daukan dogon lokacin da ya yi na fafutukar samun shugabanci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, 2022
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, 2022 © Bashir Ahmad
Talla

Baba Ahmed ya ce fahimtar shugaban ita ce da zaran ya samu mulki, matsalolin da suka addabi Najeriya za su kau, ba tare da fahimtar irin kalubalen da ke kasar ba, da kuma nazari kan hanyoyin da za a bi domin shawo kansu.

Kakakin wanda ke amsa tambayoyi a tashar talabijin ta Trust TV ya ce akwai alamun cewar Buhari na tunanin cewar 'yan Najeriya za su ji tsoronsa wajen yin duk wani abin da ya umurce su, saboda baya satar dukiyar kasa, abin da yake gani zai hana cin hanci da rashawa.

Baba Ahmed ya ce wannan tunanin na shugaban, na nufin cewar ba zai bada damar wargi ba, kuma matsalar tsaron da ya gada za ta kau baki daya, ba tare da tinkarar ta kai-tsaye ba.

Kakakin ya ce matsayin Buhari na rashin shirya yadda zai gudanar da mulkin ya fara nunawa lokacin da ya kwashe watanni kafin kafa gwamnati tare da bai wa ministoci mukamai domin su taimaka masa.

Baba Ahmed ya kuma ce, abin takaici da ya tashi nada ministocin, sai ya zabo na kusa da shi da wadanda yake dasawa da su, kana ya bar su a ofis har zuwa wannan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.