Isa ga babban shafi

Hare-haren 'yan bindiga ya kashe mutane 465 cikin wata guda a Najeriya

Daya daga cikin kungiyoyin farar hular da ke bibiyar lamurran tsaro a Najeriya mai suna “Connected Development” ta ce akalla mutane 465 ‘yan ta’adda suka kashe tare da yin garkuwa da wasu mutanen 355 a fadin Najeriya cikin watan Yunin da ya gabata.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Yayin gabatar da rahoton da aka wallafa jiya Laraba a birnin Abuja fadar gwamnatin Najeriyar, babban jami'in bincike da tsare-tsare na kungiyar farar hular ta “Connected Development” Ani Nwachukwu, ya ce baya ga dimbin rayukan da suka salwanta, mutane dubu 2,000 akasarinsu daga yankunan karkara sun rasa matsugunansu, yayinda wasu 120 suka samu raunuka daban-daban, a hare-haren da suka rutsa da su.

Rahoton ya kuma koka kan yadda a cikin shekarun da suka gabata, gwamnatin Najeriya ta kara yawan kudaden da ake kashewa don karfafa sojojinta da sauran ayyukan inganta tsaro a kasar, amma duk da haka ba a samu saukin hare-haren ‘yan ta’adda yadda ake sa rai ba.

A cikin watan Yulin da ya gabata ne dai wani bincike da jaridar Premium Times a Najeriya ta yi ya bayyana cewar, ‘yan ta’adda sun kashe jami’an ‘yan sanda akalla 65, da sojoji 81, da jami’an NDLEA biyu, sai kuma jami’an Civil Defence 5 da kuma ma’aikatan hukumar kiyaye hadurra ta FRSC 2, daga watan Janairu zuwa Yunin shekarar da mu ke ciki.

Sakamakon binciken da aka tattara daga rahotannin kafafen yada labarai, ya nuna cewa an samu asarar dubban rayuka a rabin farkon shekarar 2022, inda kimanin mutane 3,000 suka mutu a cikin watanni uku na farkon shekarar, ciki har da jimillar jami'an tsaro 157 da ‘yan ta’adda suka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.