Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta rufe kamfanonin takin bogi a Kano

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewar ta rufe wasu kamfanonin sarrafa takin zamani na bogi guda 4 da ke aiki a Jihar Kano tare da kwace motoci dauke da gurbataccen takin.

Manoma na yawan korafi kan sayar musu da takin bogi
Manoma na yawan korafi kan sayar musu da takin bogi AFP - PHILIPPE DESMAZES
Talla

Jami’an ma’aikatan gona na tarayya da ke sanya ido akan kamfanonin takin suka gano wadannan kamfanoni da ke sarrafa takin ba tare da izini ba da kuma gurbata shi da sinadarai marasa inganci suka kuma sayar wa manoma a jihar.

Gwamnatin ta bayyana sunayen wadannan kamfanoni da ta ce ta rufe da suka hada da ‘Albarka Agro-Allied and Chemical Fertilizer’ da ‘Nagarta Agro Fertiliser da suke unguwar Zara a Karamar Hukumar Kumbotso.

Sauran sun hada da kamfanin Samu Alheri da ke Jido a Dawakin Tofa da wani shagon sayar da takin da ke Getso a karamar hukumar Gwarzo.

Daraktan ma’aikatar noman da ke sanya ido akan ingancin takin zamani da kayan gona, Oke Sunday ya ce gudanar da bincike a irin wadannan kamfanoni ya zama wajibi saboda korafin da manoma ke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.