Isa ga babban shafi

Hukumar kula da kafofin yada labarai a Najeriya NBC ta soke lasisin tashoshi 52

Hukumar kula da kafofin yada labarai a Najeriya NBC ta soke lasisin tashoshin talabijin na AIT da STV baya ga wasu 50 na daban ciki har da gidajen Radio a sassan kasar sakamakon gazawa wajen sabunta lasisin yada shirye-shiryensu.

Tambarin hukumar NBC a Najeriya.
Tambarin hukumar NBC a Najeriya. © National Broadcasting Comission
Talla

Da ya ke jawabi a Abuja biyo bayan soke lasisin kafofin har guda 52, shugaban hukumar ta NBC Malam Balarabe Shehu Ilelah ya ce dukkanin tashoshin sun gaza biyan kudin sabunta lasisin inda gwamnati ke binsu bashi tun shekarar 2015.

A cewar Ilelah zuwa yanzu gwamnati na bin tashoshin 52 bashin kusan Naira biliyan 2 da miliyan 600.

Shugaban na NBC ya ce tun cikin watan Mayun da ya gabata, hukumar ta fitar da jerin sunayen tashoshin da basu sabunta lasisin na sub a tare da basu wa’adin makwanni biyu kan su sabunta lasisin ko kuma su fuskanci datsewa.

Ilelah ya ce watanni 3 bayan basu wa’adin tashoshin 52 sun gaza sabunta lasisin dalilin da ya sanya katse su a yau juma’a wanda ke nuna soke lasisin yada shirye-shiryensu bisa amfani da tanadin doka mai lamba CAPN11 karkashin sashe na 10(a) na kundin tsarin mulkin na 2004.

Tashoshin da wannan soke lasisi ya shafa kamar yadda hukumar ta fitar da jadawalinsu sun kunshi Silverbird TV mai dauke da tashar redio ta Rhythm FM sai gidan talabijin na AIT da Radiyon Ray Power kana Greetings FM da Tao FM sannan Zuma FM da kuma Crowther FM da We FM baya ga Bomay Broadcasting Services.

Sauran sun kunshi MITV da Classic FM da Classic TV kana Beat FM da Splash FM da kuma Rock City FM da Family FM da kuma Space FM sannan Radio Jeremi.

Karin tashoshin da suka fuskanci wannan soke lasisi akwai  FM Abuja da FM Lagos da FM Yenagoa

da FM Port-Harcourt da FM Jos da kuma Wave FM da gidajen Radiyo mallakin jihohin Kogi da Kwara State da kuma Neja.

Akwai kuma gidajen Radio na Benin Network da FM Network da FM Okene kana FM Suleja da FM Abuja da FM Benin da Breeze FM sai kuma Vibes FM da Family Love FM kana gidajen Radiyon Port-Harcourt da na Gombe da na Lagos da Osun da kuma na Ogun da Ondo da Rivers da Bayelsa da Cros River da Imo da Anambra da Borno .

Sauran sun kunshi gidajen Radiyon jihohin Yobe da Sokoto da Zamfara da Kebbi da Jigawa da Kaduna da Katsina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.