Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 115 tare da raba iyalai dubu 73 da muhallansu a Najeriya

A karon farko fadar shugaban Najeriya ta fitar da alkaluman mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a sassan kasar, inda ta bayyana cewa, daga watan Janairu zuwa yanzu ambaliyar ta kashe mutane 115, tare da jikkata wasu 277 gami da raba wasu dubu 73 da 379 da muhallansu a jihohi 22 da kuma birnin Abuja.

Ambaliyar ruwa na ci gaba da illa a sassan Najeriya.
Ambaliyar ruwa na ci gaba da illa a sassan Najeriya. JUNIOR D.KANNAH / AFP
Talla

Yayin da ya ke karin haske kan bayanan ma’aikatun gwamnati da hukumomin da abin ya shafa suka fitar a jiya, mai magana da yawun shugaba Muhammad Buhari, Garba Shehu, ya ce ambaliya da kuma ruwan sama mai karfin gaske ya yi sanadiyyar lalata gidaje kimanin dubu 37 da 633.

Ya kara da cewa tun daga farkon shekarar nan an samu rahoton ambaliyar ruwa a jihohi da dama wadanda daga cikinsu suka hada da Lagos da Borno da Taraba da Adamawa baya ga jihar Edo.

Sauran jihohin sun kunshi Delta da Kogi da jihar Niger baya ga Kano da Jigawa, ibtila’in da ya shafi mutane dubu 508 da 721.

Kakakin shugaban Najeriya ya ce gwamnati za ta ci gaba da sanya ido kan abinda ke faruwa da kuma hada gwiwa da gwamnatocin jihohi da al’ummomin da abin ya shafa don rage illar ibtila’in, da kuma samar da kayayyakin bukata.

Babban jami’in ya ce shugaba Buhari ya bukaci mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su rika bin shawarwarin gargadin farko da kwararru ke yi, wadanda ke sa ido kan yanayi da kuma ayyukan agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.