Isa ga babban shafi

Takaddama ta kaure tsakanin Kwastam da NNPC akan yawan man da Najeriya ke fitarwa

Yanzu haka takaddama ta kaure a Najeriya tsakanin shugaban hukumar kwastam Kanar Hameed Ali mai ritaya da shugabannin kamfanin man kasar na NNPC dangane da gaskiyar yawan man da Yan kasar ke sha kowacce rana.

Wani gidan man Najeriya da yayi ambaliya a yankin Neja Delta 18/06/17.
Wani gidan man Najeriya da yayi ambaliya a yankin Neja Delta 18/06/17. REUTERS - Stringer .
Talla

Yayin da kamfanin NNPC ke cewa a kowacce rana jama’ar kasar na shan man fetur da yawansa ya kai lita miliyan 60, shugaban kwastam yace ya dace kamfanin yayi bayani dangane da yadda akeyi da lita miliyan 38 daga cikin lita miliyan 98 da ake fitarwa daga rumbunan sa kowacce rana.

Ali ya tambayi kwamitin Majalisar wakilai da ya taimaka wajen gano amsa daga NNPC yadda akeyi da lita miliyan 38 da kamfanin ke bada damar dauka kowacce rana, saboda cewar da yayi lita 60 kawai ake sha a cikin kasar, kuma gwamnati na sanya tallafi akan kowacce litar da ake sayarwa a cikin gida.

Shugaban hukumar yayi watsi da zargin cewar ana safarar man zuwa kasashen ketare ta kan iyakokin kasar da jami’an sa ke sanya ido, yayin da ya tambayi hanyar da ake bi da kuma yawan motocin dake fitar da lita miliyan 38 suwa kasashen ketare.

An dade ana zargin cewar wasu bata gari daga cikin jami’an gwamnati da yan kasuwa na safarar man zuwa kasashen dake makotaka da Najeriya saboda sayar da shi a farashi mai tsada sakamakon tallafin da gwamnati take zubawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.