Boko Haram ta kashe masu ibada a Masallacin Borno
Mayakan Boko Haram sun kai hari a wani Masallaci da ke jihar Borno ta Najeriya, inda suka kashe babban limamin Gima tare da karin wasu masu ibada.
Wallafawa ranar:
Kazalika harin wanda ya auku a ranar Juma’a, ya kuma raunata mutane da dama, yayin da ‘yan ta’addar suka mamaye garin Ngulde da ke Karamar Hukumar Askira -Uba ta jihar Bornon.
Mayakan da yawansu ya kai 20, sun kai farmakin ne a sanyin safiyar ranar ta Juma’a , inda suka yi ta bude wuta kan mutanen da suka kammala sallar Asuba a Masallacin.
Har ila yau, mayakan sun yi awon gaba da dabbobi da abinci, sannan suka cinna wa wasu motoci wuta a garin na Ngulde wanda ke kusa da dajin Sambisa.
Boko Haram na ci gaba da kisan mutane babu kakkautawa a Najeriya duk da ikirarin gwamnatin kasar na samun galaba a kan mambobin kungiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu