Isa ga babban shafi

Hukumar SSS ta gano kakin Soji da makudan kudade a gida da Ofishin Tukur Mamu

Hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta sanar da samun tarin kakin Soji da makudan kudade a gida da ofishin Tukur Mamu yayin sumamen da suka kai masa.

Tukur Mamu dan jaridar da ke shiga tsakani don sakin fasinjan da 'yan bindiga ke garkuwa da su.
Tukur Mamu dan jaridar da ke shiga tsakani don sakin fasinjan da 'yan bindiga ke garkuwa da su. © Vanguard
Talla

Gano wadannan kayaki na zuwa ne bayan kame Tukur Mamu mawallafin jaridar Desert Herald a larabar da ta gabata, lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano.

Dan jaridar wanda shi ne kakakin shehin malamin nan, Dr Ahmed Gumi, shi ke matsayin mai shiga tsakanin don sakin fasinjan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da ‘yan bindigar daji suka yi garkuwa da su tun cikin watan Maris din shekarar nan.

Tun farko jami’an ‘yan sandan kasa da kasa ne suka kame Tukur Mamu a Masar lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Umara kasar Saudiyya dalilin da ya sanya dawo da shi Najeriya don amsa tambayoyi daga jami’an tsaro.

Sanarwar da SSS ta fitar dauke da sa hannun kakakinta Peter Afunanya, ta ce hukumar ta gano kayakin laifuka a gida da kuma ofishin dan jaridar, bayan gudanar da sumame.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.