‘Yan sanda 3 sun mutu a harin da 'yan bindiga suka kai wa wani Sanata a Najeriya
Wasu ‘yan sanda sun gamu da ajalinsu a a jiya Lahadi sakamakon harin da ‘yan sanda suka kai wa wani dan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ifeanyi Ubah, wanda ke wakiltar mazabar Anambra ta Kudu.
Wallafawa ranar:
‘Yan bindigar sun kai wa ayarin sanatan harin ne a kauyen Enugwu-Ukwu a karamar hukumar Njikoka ta jihar Anambra.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun yi wa ayarin na Uba kwanton bauna ne, inda suka bude musu wuta, har suka kashe ‘yan sandan da ba a kai ga tantance adadinsu ba da ke tsaron lafiyar dan majalisar.
Wata majiya ko ta ce tun da farko ‘yan sandan sun tinkari ‘yan bindigar, inda suka yi musayar wuta amma duk da haka 3 daga cikin jami’an suka mutu.
Da aka tun tube shi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da harin a kan sanatan,amma ya ce ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu