Isa ga babban shafi

Najeriya: Yadda ma'aikatan hukumar fansho ke karbar naira miliyan 3 kowanne wata

Hukumar dake kula da kudaden fanshon 'yan Najeriya da ake kira PenCom tayi watsi da rahotan dake bayyana cewar kowanne ma’aikacin ta na karbar naira miliyan 3 kowanne wata a matsayin albashi.

Aisha Dahir Umar, shugabar hukumar PENCOM ta Najeriya
Aisha Dahir Umar, shugabar hukumar PENCOM ta Najeriya © punch
Talla

Watsi da wannan rahoto ya biyo bayan binciken da kwamitin kudi na majalisar wakilan Najeriya keyi, wanda ya bukaci bayani akan yadda Hukumar ke biyan kowanne ma’aikaci naira miliyan 2 da dubu 400 kowannne wata a matsayin albashi, kamar yadda takardun da Hukumar ta gabatar musu ya nuna.

'Yan majalisar sun bayyana matukar bacin ransu da yadda ma’aikata a Hukumar zasu dinga karbar wadannan makudan kudade a matsayin albashi, yayin da wasu ma’aikatan da suka aje aikin su ke mutuwa ba tare da sun karbi kudaden fanshon su ba.

Kokarin shugabar Hukumar PenCom Aisha Dahir-Umar na yiwa 'yan majalisun gamsassun bayanai yaci tura, abinda ya sa kwamitin ya baiwa Hukumar umurnin komawa domin kawo cikakkun bayanai akan albashin ma’aikata 500 dake aiki tare da ita.

Wannan ya sa kafofin yada labarai wallafa labarin yadda Hukumar ke biyan ma’aikata albashin da ya wuce kima, yayin da ita Hukumar ta fitar da sanarwar dake watsi da albashin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.