Isa ga babban shafi

Kotu a Najeriya ta umarci malaman jami'o'in kasar su janye yajin aiki

Kotun ma’aikata ta Najeriya da ke Abuja ta umarci kungiyar malaman jami’o’in kasar, da ta janye yajin aikin da take yi.

Yajin aikin malaman jami'a a Najeriya ya jefa dalibai cikin yanayi maras dadi
Yajin aikin malaman jami'a a Najeriya ya jefa dalibai cikin yanayi maras dadi Premium Times Nigeria
Talla

Mai shari’a Polycarp Hamman ta ce yajin aikin ya saba wa sashe na 18 (1) (2) na dokar aiki, wanda ya haramta yajin aikin nasu.

Hamman ta bayyana cewa yajin aikin ya haifar da barnar da ba za a iya misalta ba ga rayuwar dalibai da dama a Najeriya.

Mai shari’a Hamman ta mika karar zuwa ga shugaban kotun domin a sake masa mukami.

A ranar 14 ga Fabrairu, 2022, ASUU ta tsunduma yajin aikin neman a sake tattaunawa kan yarjejeniyar da suka kulla da gwamnati a 2009, da dai sauransu.

Tattaunawar da aka yi tsakanin ASUU da gwamnati ba ta haifar da sakamako ba, abin da ya sanya daga bisani gwamnatin Najeriya maka ASUU gaban kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.