Isa ga babban shafi

'Yan sanda Najeriya sun kwace ababen hawa da ake amfani da su wajen satar danyen mai

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce jami’anta na musamman da ke dakile satar man fetur da sauran albarkatunsa, ta kwace ababen hawa 123 da suka hada da tankoki, manyan motoci, da kuma jiragen ruwa, wadanda ake amfani da su wajen satar dake addabar tattalin arzikin kasar.

Wani wajen tace danyan man fetur ba bisa ka’ida ba a kudancin Najeriya.
Wani wajen tace danyan man fetur ba bisa ka’ida ba a kudancin Najeriya. © REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Yayin da ya ke karin bayani kan nasarar da suka samu, Sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya ce, rundunar ‘yan sandan ta kama lita 1,301,020 na Gas, da lita 135,000 na danyen mai, sai lita 4,900 na tataccen man fetur, da kuma lita 45,000 na bakin mai.

Cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriyar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce yanzu haka an gurfanar da mutane 52 a fadin kasar, akan laifukan da suka shafi satar dan mai da sauran albarkatunsa.

A cikin watan Yulin shekarar 2020, Kamfanin Man Najeriya NNPC ya ce, kasar ta yi asarar kudin da ya kai Dala miliyan 48 ko kuma Naira biliyan 17 saboda satar mai a shekarar, matsalar da har yanzu mahukuntan Najeriyar ke kokawa akai, la’akari da yadda take cigaba da shafar tattalin arzikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.